25 Maris 2021 - 13:45
Iran Ta Caccaki Hukumar IAEA Game Da Yarjejeniyar Nukiliya

Wakilin Iran, a kungiyoyin kasa da kasa dake birnin Vienna, Kazem Gharibabadi, ya caccaki shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, Rafael Grossi, game da firta wasu kalamai marasa digi game da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran a 2015.

ABNA24 : M. Gharibabadi, ya ce kalamman baya bayan nan na Rafael Grossi, ba zasu haifar da da mai ido ba game da yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Ya kara da cewa irin wadannan kalamman, kan iya zubar da kimar wannan hukuma a idon Iran, wanda kuma nakaso ne ga alakar dake tsakanin Iran da kuma hukumar inji shi.

Dama dai a cewarsa yarjejeniyar tana cikin tsaka mai wuya, kenan ba lokaci ne ban a kara dagula al’amura, kamar yadda wakilin na Iran a Vienna, Kazem Gharibabadi, ya fadawa ‘yan jarida.

342/